Thursday, October 13, 2016

LABARI DA DUMIDUMINSA!!!: An sako 21 daga cikin 'Yan matan Chibok wa'enda Boko Haram suke garkuwa da su




21 daga cikin 'Yan matannan na Chibok da yan boko-haram sukayi garkuwa da su, an sako su
Wanda wasu kafofin yada labarai sun rawaito cewa hakan ya biyo bayan sake wasu daga cikin 'yan uwansu da gwamnatin Najeriya take tsare dasu
Amma gwamnatin Najeriyan ta bakin ministan yada labarai sun musanta hakan. 
Tuni dai aka deba yan matan a jirgin sama zuwa Maiduguri dan duba lafiyarsu 

Monday, October 10, 2016

'YAN SANDA SUN CAFKE WASU MUTANE BIYU DA DAKAKKEN KAN MUTANE A IPAJA NA JAHAR LAGAS



__________________________________________ 'Yan Sanda sun kama Jamiu Alabi 'dan shekara 24,da kuma Yemi John' yar shekara 32 cikin dare da dakakken kanyin mutane da suka shiryashi a cikin Buredi (Bread).

 Wannan lamari ya faru ne ranar Asabar 'dinnan daya wuce a Church Bus Stop cikin Ipaja dake jihar Lagas
 Wa'enda aka kaman dai sun shirya dakakken kayukanne a cikin Leda sai suka sanya salitep da rubuta suna kamar haka a jikin kowani daya kaman haka; Danjumo N20,000, Yusuf N70,000 da kuma Alhaji Mumuni N10,000

 Mai magana da yawun 'yan Sanda Superintendent(SP) Dolapo Badmos, ya baiyana cewa ananan ana kan tsastsauran bincike akan wannan lamari

 Ya kuma 'kara baiyana cewa akwai 'yan fashi da makami da akayi nasaran cafke su a hanyan Shibiri/Imude zuwa Ojo, bayan sun yiwa wata mata mai suna Ifeoluwa Francis fashi.
 Segun Ariyo dan shekaru 17 da Michael Adetona dan shekaru 16, tace sun 'kwace mata N20,000, da BlackBerry Z3 da kuma recharge cards. Badmos tace an cafke sune sa'ilin da suke 'kokarin rabawa.

Thursday, October 6, 2016

ZIYARAN GWAMNA KASAR CHINA KWALLIYA ZA TA BIYA KUDIN SABULU!




Daga Balarabe Shehu Ilelah
______________________________________________
A sakamakon ziyarar da gwamnan Jihar Bauchi M A Abubakar Esq, ya kai china, wata tawagar kwararru kan aikin noma wadanda kuma ke da sha'awar zuba jari a aikin gona ta iso Bauchi domin ziyarar gani da ido . makasudin zuwansu dai shi ne 1. ganin filayen noma da jihar bauchi ke da su domin su bude katafaren gonan noman abubuwa daban daban a jihar Bauchi, sannan su taimaka wajen hadinguiwa da manomanmu da kuma horas da su hanyar noman zamani ta yadda Jihar Bauchi za ta yi fintinkau wa sauran jihohi wajen aikin gona a Nijeriya. tawagar ta ziyarci  wani makeken filin noma a gadar maiwa da Giwo Farms a Alkaleri inda ta ga gonakin kankana da gyada da masara da shinkafa da sauransu .2. tawagar na da sha'awar karbar kamfanin nama na Bauchi domin sake farfado da shi kuma ta ziyarci kamfanin naman a Bauchi .3 Tawagar ta ziyarci kamfanin yin takin zamani na Bauchi , a nan ma ta nuna sha'awarta na karbar wajen domin  farfado da shi da kuma bunkasa shi ta yadda za ta samar da takin zamani  Nijeriya baki daya. Wadanda suke zagawa da  tawagar ta mutanen  kasar China sun hada da  Eng Habu Mamman  da Kwamishina aikin gona na jiha da Gneral Manager  na Kamfanin nama na bauchi Dr. Kassim da  Manajojin aikin gona  Alhaji Sade da Yariman Gital  da Shugaban kamfanin zuba jari na Bauchi da dai sauran wadanda Gwamanan ya wakilta. Za mu cigaba da kawo muku ayyukan da  tawagar ke yi na ziyarce ziyarce a Bauchi. Allah sa wannan ziyarar ta amfani al'ummar jihar Bauchi da Nijeriya baki daya.

Monday, October 3, 2016

AN SAKE SAMUN ZUNZURUTUN KUDI DALA MILIYAN TALATIN ($30M) A WANI SABON ASUSUN AJIYA NA UWAR-GIDAN. TSOHON SHUGABAN KASA PATIENCE JONATHAN



A wani sabon labari da muka samu daga shaharenren camfanin labaran nan na saharareporters, sun baiyana cewa an samu wani sabon asusun ajiya na banki dake da alaka da matan tsohon shugaban kasa Patience Jonathan da zunzurutun kudi dala miliyan talatin ($30M).
 Wannan labari yana zuwa ne jim kadan bayan dawowansu daga kasan waje, yanda suka sauka da mijinta a filin jirgin sama dake jihar Port Harcourt domin karasawa Jihar Bayelsa.
Tsohuwar first ledin dai hukumar EFCC tana tuhumarta da almundahana, wanda hakan ya janyo rufe wasu asusun ajiyanta na banki da kuma wasu kaddarori.

Saturday, October 1, 2016

HAUSA TA SAMU CI GABA A DUNIYA!, "NA KARA YAREN HAUSA A FACEBOOK" INJI MARK ZUCKERBERG

_____________________________________________



Me kamfanin nan na Facebook (Mark Zuckerberg) ya baiyana cewa ya kara yaren  Hausa da Fula a jerin yaru-rukanda suke camfanin nasa.
A jiya Jumma'a ne ya kara yaru-rukan tare da wasu guda biyu wato yaren Maltese da Corsican, a yanzu dai facebook tana amfani da yaru-ruka sama da dari (100).

A ranar Jumma'a 2 ga watan satumba ne Mark Zuckerberg yakai ziyara fadar shugaban kasa domin ganawa da shugaba Muhammadu Buhari.

 A sanarwansa jiya Zuckerberg ya baiyana cewa wannan kari zai farfado da bacewan wa'ennan yaru-ruka a idan duniya. “Facebook is now available in more than 100 languages — with more than one billion people using a language other than English! Today we added Hausa, Fula, Maltese and Corsican.” “Our community makes this possible. Over the last decade, hundreds of thousands of people around the world have worked together to find the right translations for words and phrases in the Facebook interface. Because the idea of a “Like” in English may mean something different in Arabic or Japanese.”
"For people to share what matters to them and see what matters to the people they care about, they need services available in a language they know. Some of the languages we’ve added don’t have meaningful presence on the internet.” “Others, like Corsican, are in danger of disappearing altogether, according to UNESCO.”
Ya karasa da cewa “So thanks to everyone in our community for helping us hit this milestone of 100 languages! We’ll keep working to open up our community to everyone – no matter where they live or what language they speak.”

Hausa da Fula (wato Fulani) a turanci ana kiransu Chadic language (reshen Afroasiatic language family) da non-tonal languages wanda akwai mutane sama da miliyan hamsin (50m) masu magana da harshen a sama da kasa 20 dake nahiyan afrika.

Idan za'a iya tunawa Zuckerberg lokacin ziyaran sa Nijeriya ran talatin(30) ga watan Agusta, sa'ilin ganawa da masu amfani da sarrafa na'uran comfuta a jahan Legas, yayi alkawarin yin amfani da yarukan Najeriya a dandalin sadarwa na Facebook.  Zuckerberg also reiterated this resolve to make the platform available to people no matter where they are on the globe.

Tuesday, September 27, 2016

N-POWER PROGRAMME: IDAN KANA DA DAMUWA AKAI, TO GA YANDA ZAKA WARWARE TA!!!



Kana daga cikin mutanen da suka sami matsala a N-Power portal? Ga abinda mutanen N-Power suke cewa a shafin su na Facebook page:

"Idan kayi registered da NPower TEACH, kuma ranar da suka ware zaka yi assessment ya wuce baka iya kayi log in ba, ambaka daman da zaka tura sako ta INBOX a (N-power Facebook page) a jere kamar haka. 

1. CIKAKKEN SUNANKA DA KAYI REJISTA
2. ADRESHIN KANA EMAIL
3. NOMBAN WAYA


Mun kuma lura dayawan mutane basu iya tuna mukamin da suka nema a (N-Power).
Idan kana daga cikin su, ka turo sako ta INBOX kamar haka. 

1. Unsure
2. SUNA
3. ADRESHIN EMAIL
4. NOMBAN WAYA."



Ka ziyarci shafinsu na Facebook  anan https://www.facebook.com/npowerng/  domin tura sakon ta direct message.

Allah ya bada sa'a! 

Saturday, September 17, 2016

WITHOUT A DOUBT, ONE OF THE BEST THINGS TO HAPPEN IN NIGERIA



FG To Drive “Change Begins With Me” In Civil Service

Civil-Servants-Winifred Oyo-Ita-change begins with me
Head of Service of the Federation, Mrs Winifred Oyo-Ita
The Head of Service of the Federation, Mrs Winifred Oyo-Ita, says the Federal Government will drive the recently launched “change begins with me” project in civil service.

Mrs Oyo-Ita explained that the reason for the development was to change the orientation of the public servants towards work.

She made the remarks on Wednesday in an interview with Channels Television in Abuja, Nigeria’s capital while reacting to the number of civil servants that resumed work after the Eid-el-Kabir holidays.

The Head of Service expressed satisfaction over the way workers’ attitude to work had changed, noting that many civil servants were already buying into the new national orientation programme, despite Nigeria’s current economic challenges.

She stated that the government would work towards establishing a reward mechanism for public servants, in order to drive the project in the service.

President Muhammadu Buhari launched the “Change Begins With Me”, as part of his administration’s strategy to carry all Nigerians along on the journey to a better and greater society that everybody could be proud of.

He said that the programme was the best way to sustain the effort his administration had made in the fight against corruption.