Monday, October 3, 2016
AN SAKE SAMUN ZUNZURUTUN KUDI DALA MILIYAN TALATIN ($30M) A WANI SABON ASUSUN AJIYA NA UWAR-GIDAN. TSOHON SHUGABAN KASA PATIENCE JONATHAN
A wani sabon labari da muka samu daga shaharenren camfanin labaran nan na saharareporters, sun baiyana cewa an samu wani sabon asusun ajiya na banki dake da alaka da matan tsohon shugaban kasa Patience Jonathan da zunzurutun kudi dala miliyan talatin ($30M).
Wannan labari yana zuwa ne jim kadan bayan dawowansu daga kasan waje, yanda suka sauka da mijinta a filin jirgin sama dake jihar Port Harcourt domin karasawa Jihar Bayelsa.
Tsohuwar first ledin dai hukumar EFCC tana tuhumarta da almundahana, wanda hakan ya janyo rufe wasu asusun ajiyanta na banki da kuma wasu kaddarori.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment