Friday, October 28, 2016

Aure a gidan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari . 
__________________



A gobe Assabar 29/10/2016 ne a ke sa ran gabatar da Daurin Auren Ýar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari , alamu na nuna cewa Daura zata yi cikar Kwari .

Wannan dai shi ne a Karon farko tun bayan rantsar da shi a matsayin Shugaban Najeriya a shekarar da ta gabata 2015 , tun safiyar yau din nan Manyan Mutane a ko ina a fadin Najeriya ke tururuwa don halarta wannan Aure .

Ita dai Fatima Ýa ce ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Matar sa ta farko ta haifa masa Marigayiya Hajiya Safinatu Buhari , Shugaban Bankin bada rancen Gidaje na gwamnatin tarayya shi ne zai kasance Angon ta Mal . Gumba Ya'u Kuma .

Allah yasan ya albarka cikin wannan Aure .

No comments:

Post a Comment