Monday, October 10, 2016
'YAN SANDA SUN CAFKE WASU MUTANE BIYU DA DAKAKKEN KAN MUTANE A IPAJA NA JAHAR LAGAS
__________________________________________ 'Yan Sanda sun kama Jamiu Alabi 'dan shekara 24,da kuma Yemi John' yar shekara 32 cikin dare da dakakken kanyin mutane da suka shiryashi a cikin Buredi (Bread).
Wannan lamari ya faru ne ranar Asabar 'dinnan daya wuce a Church Bus Stop cikin Ipaja dake jihar Lagas
Wa'enda aka kaman dai sun shirya dakakken kayukanne a cikin Leda sai suka sanya salitep da rubuta suna kamar haka a jikin kowani daya kaman haka; Danjumo N20,000, Yusuf N70,000 da kuma Alhaji Mumuni N10,000
Mai magana da yawun 'yan Sanda Superintendent(SP) Dolapo Badmos, ya baiyana cewa ananan ana kan tsastsauran bincike akan wannan lamari
Ya kuma 'kara baiyana cewa akwai 'yan fashi da makami da akayi nasaran cafke su a hanyan Shibiri/Imude zuwa Ojo, bayan sun yiwa wata mata mai suna Ifeoluwa Francis fashi.
Segun Ariyo dan shekaru 17 da Michael Adetona dan shekaru 16, tace sun 'kwace mata N20,000, da BlackBerry Z3 da kuma recharge cards. Badmos tace an cafke sune sa'ilin da suke 'kokarin rabawa.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment